1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An ceto daruruwan bakin haure a cikin teku

Usman ShehuNovember 1, 2014

Hukumomin kasar Italiya sun bayyana cewa wani jirgin kwale-kwale da ke dauke da bakin haure ya yi hatsari a gabar ruwan kasar, inda aka ceto yan gudun hijara da dama.

https://p.dw.com/p/1Dfbu
Symbolbild Flüchtlinge Mittelmeer Bootsflüchtlinge Migranten
Hoto: picture-alliance/dpa

Sama da bakin haure 200 aka ceto a gabar ruwan kasar ta Italiya, wannan ya faru ne kwana guda bayan fara aikin rundunar Tarayyar Turai ta musamman, wajen kula da yan gudun hijira dake tsallakowa ta gabar ruwa.

A halin da ake ciki kuwa jami'an tsaron kasar Italiya sun cafke wani dan kasar Ghana da ake zargi da safarar mutane, wanda ake cewa yana da hannu a jigilar jirgin ruwan da ya nitse da bakin haure a ranar Alhamis ta gabata, inda yanzu sojojin ruwan Italiya suka gano mutane 90, wasu kimanin 25 kuwa sun bace.

Kungiyar Tarayyar Turai dai ta kafa wata sabuwar runduna da aka sawa suna Triton, don yin sintiri a gabar ruwan kasashen, musamman inda 'yan gudun hijira suka saba tsallakowa don shiga Turai.