1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 27 sun kubuta daga masu garkuwa a Najeriya

Abdul-raheem Hassan
May 9, 2019

'Yan sanda a Najeriya sun kubutar da mutane 27 da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su har da wasu 'yan kasar China biyar, an kuma kashe wasu daga cikin masu satar mutanen.

https://p.dw.com/p/3IFm0
Nigeria Polizei
Hoto: Getty Images/AFP/P. Utomi Ekpei

A cikin wata sanarwar da rundunar 'yan sandan suka fitar, sun ce mafi yawan wadan da aka kubutar 'yan jihar Zamfara ne da ke arewa maso yammacin kasar. 'Yan sandan sun tabbatar da bindige biyu daga cikin masu garkuwan.

Nasarar kubutar da mutanen ta zo ne a dai dai lokacin shugaban 'yan sandan Najeriyar Mohammed Abubakar ya kaddamar da sabbin dabarun tinkarar ayyukan ta'addanci da masu satar mutane a kasar.

Rahotannin jami'an 'yan sandan Najeriya na cewa cikin watanni hudun farko na shekarar 2019, mutane 270 ne aka kama bisa zargin satan mutane domin samun kudin fansa.