1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An dakatar da Rasha daga wasannin Olympic na nakasassu

Gazali Abdou TasawaAugust 7, 2016

Kwamitin shirya wasannin Olympic na nakasassu wato IPC ya sanar a wannan Lahadi da dakatar da Rasha daga shiga wasannin Olympic na nakasassu na daga bakwai zuwa 18 ga watan Satumba mai zuwa.

https://p.dw.com/p/1Jd7a
Russland Fechten Paralympics 2016
Hoto: picture-alliance/dpa/V. Gerdo

Shugaban kwamitin na IPC Philip Craven ya ce sun dauki wannan mataki ne a bisa la'akari da sakamakon kwamitin bincike na McLaren wanda ya bankado badakalar amfani da haramtattun kwayoyi masu kara kuzari da 'yan wasan kasar Rasha da suka hada da nakasassu suka yi amfani da su a wasannin Olympic na shekara ta 2014 a kasar ta Rasha.

Sai dai tuni ministan wasannin motsa jiki na kasar Rasha Vitali Moutko ya soki lamirin matakin wanda ya ce ya wuce hankali.Kasar rashar na da wa'adin wata guda domin dauka kara kan wannan hukunci.

A baya dai babban kwamitin shirya wasannin Olympic ya yanke shawarar bai wa kasar ta Rasha izinin halartar wasannin Olympic da ke gudana a yanzu haka a birnin Rio duk da samun Rashar da aikata wannan laifi.