1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon zaben Jihar Rivers sai an yi jigilarsa ta ruwa

Abdourahamane Hassane
March 10, 2019

Rahotannin da ke zuwa mana daga Jihar Rivers na cewar yanzu haka an dakatar da bayyana sakamakon zaben saboda yamutsin da ya taso abin da ya sa jami'an hukumar zaben ke jin tsoro kan kare lafiyarsu.

https://p.dw.com/p/3EkBD
Shugaban hukumar zaben Najeriya INEC  Prof. Mahmoud Yakubu
Shugaban hukumar zaben Najeriya INEC Prof. Mahmoud Yakubu Hoto: Imago/Zuma

Hukumar zabe ta kasa a jihar Rivers ta bayyana cewar ta dakatar da aikin karbar sakamakon zaben da ta fara tun jiya wanda zai kai ga bayyana wanda ya lashe zaben ''gwamna'' na Jihar,Hakan ta ce matakin  na da nasaba da dalilai da suka hada da barazana da rayuwarsu ta shiga a yanzu din.