1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An daure wani tshohon minista a Kamaru

August 13, 2013

Kotu ta sami Urbain Olanguena Awano da laifin hada kai da 'yan kwangila wajen karkata akalar sama da miliyan 80 na CFA lokacin da ya rike mukamin ministan kiwon lafiya.

https://p.dw.com/p/19OhH
19.02.2013 DW Online Karte Kamerun Waza National Park

Wata babbar Kotun kasar kamaru ta yanke ma wani tsohon ministan kiwon lafiyan kasar Urbain Olanguena Awono hukunci shekaru 20 a gidan yari, bayan da ta same shi da laifin sama da fadi da dukiyar kasa. Alkalin kotun da ke hukunta laifukan da ke da nasaba da ci-hanci da karbar rashwa, ya gabatar da shaidun da ke nuna cewar Olanguena Awono ya hada kai da wasu 'yan kwangila wajen karkata akalar fiye da miliyan 80 na CFA.

Tun dai shekaru biyar da suka gabata ne aka kame Olanguena Awono bayan da gwamnatin ta kaddamar da shirin rashin sani da sabo a kan duk manyan jami'anta da ke sama da fadi da dukiyar kasa. A shekarar da ta gabata ne dai shugaban Paul Biya na Kamaru ya kafa kotun musamman da ke sauraran kararrakin da ke da nasaba da cin hanci da karbar rashawa Tuni ma ta daure da dama daga cikin wadanda aka gurfanar ciki kuwa har da tsohon firaminista da ministoci da kuma manajojin kanfanoni.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Saleh Umar Saleh