1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Laberiya: Zirga-zirgar jiragen sama ta kankama

June 29, 2020

Liberia ta zama kasa ta farko a yammacin Afrika da ta bude filin jiragen samanta bayan da a baya ka rufe shi sakamakin annobar coronavirus.

https://p.dw.com/p/3eWAW
Elfenbeinküste Felix Houphouet Boigny International airport Ebola Maßnahme
Hoto: picture-alliance/dpa

Fasinjoji da ma’aikata na ta zirga-zirga a filin jirgin saman kasa da kasa a Liberia sanye da takunkumi, a gefe guda kuma an samar da wuraren wanke hannu da dama a kofofin shiga da fita, kazalika aka tilasta bada tazara  tsakanin mutane don dakile yaduwar cutar covid-19. 

Kasar Liberia dai ta bude filin jiragen saman nata ne watanni uku bayan kulle shi saboda annobar corona, matakin da ake ganin zai rage radadi ga yankin yammacin Afirka. Matafiya irinsu Regina Benson na shaukin yin balaguro bayan daukar tsawon lokaci tsugunne wuri daya.

“Ni ‘yar kasuwa ce kuma yau ya kasance ranar zagayowar haihuwata, zan je Amsterdam don yin bikin wannan rana tare da yarana. Na sami sa’ida kuma ina farin ciki wannan filin jirgen na bin dukkanin ka’idoji, don haka ina tunanin ban da wata fargaba ta yin balaguron yau." 
  
Dakatar da tashin jirage ba ga fasinjoji kadai ta shafa ba har ga ma‘aikatan filin jiragen, dawowa bakin aiki bayan shafe tsawon lokaci a gida abun farin ciki ne gare su, sai dai matakan kare kai abu ne mai mahimmaci ga lafiyarsu.

Jirgin Beijium
Jirgin Beijium Hoto: picture-alliance/dpa/N. Maeterlinck

Rose Budy Freeman dake zama mataimakiyar manajan sashin siyar da tikiti.

"Mutane na yawan kira tare da tambayar yaushe zamu koma aiki? Sai nai duk da murnar dawowa aiki amma akwai tsoro. Tsoron shi ne ba mu san mai dauke da kwayar cutar ba.“
 
Matakin bude filin jirgin saman dai ya haifar da tafka babbar muhawa a tsakanin kamfanonin jiragen saman da su yi jigilar fasinjoji don dakile yaduwarta cutar ko kuma mayar da hannun agogo baya. Babban Manajan Filin jirgin saman na Robert, Bishop J. Allan Klayee ya ce sun tattauna da kamfanonin jiragen sama don tabbatar da lafiyar fasinjoji.

Filin jirgin sama a Dakar, Senegal
Filin jirgin sama a Dakar, SenegalHoto: Getty Images/AFP/S Souici

“Akwai matakai da dama da aka dauka saboda yadda muke tafiyar da lamura, ba zai kasance kamar da ba. Muna aiki da kamfanonin jiragen sama, sun fada mana abun da za su iya muma mun kawo namu sai muka hada muka samar da dokoki daya, mafi mahimmaci da muka dauka su ne tilasta wanke hannuwa da sanya takunkumin fuska, auna dumin jiki da kuma bada tazara a tsakanin juna wanda suke da mahimmanci.“

Kamfanin jirgin kasar Brussels shi ne jirgin da zai fara sauka da misalin karfe 8 na daren litinin din nan. Matafiya da dama ne ke sa ran bin wasu jiragen a kwanaki kadan masu zuwa. Sai dai akwai fargabar cewar bude filin jiragen da kasar Liberia ta yi ka iya zama babbar barazana na karuwar adadin masu dauke da cutar corona a kasar.