1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara kada kuri'a a kasar Amirka

November 6, 2012

Jihohi biyar na kasar Amirka sun fara kada kuri’a da nufin zaben shugaban kasa da kuma 'yan majalisa. Obama da Romney na tafiya kafada da kafada a zaben Dixville na Hamshire.

https://p.dw.com/p/16dZi
A jihar Ohio ma an fara zabeHoto: Reuters

Dubun dubatan amurkawa sun fara kada kuri'a da nufin zaben sabon shugaba tsakanin Barack Obama na jam'iyar Democrate da kuma dan takarar Republican Mitt Romney. Tun da misalin karfe 11 agogon Najeriya ne wadanda suka cancanci kada kuri'a suka yi dafifi a gaban runfunan zabe na jihohi biyar na Amirka da suka hada da New Jersey da kuma New York domin zaben 'yan takarar da suka ka sun dace. In anjima ne sauran jihohin za su bi sahu domin bai wa Amirkawa miliyon 200 damar kada Kuri'ansu domin zaben shugaba kasa da kuma 'yan majalisan dokoki da kuma dattijai.

Sai dai kuma kamar yadda aka saba bisa al'ada, mazauna garin Dixville da ke cikin jihar New Hamshire sun riga sun kada kuri'unsu tun da 12 dare. Sakamakon farko da aka samu ya nunar da cewar 'yan takarar biyu wato Obama da kuma Mitt Romney suna tafiya kafada da kafada inda kowannensu ya samu kashi 50 daga cikin 100 na kuri'un da aka kada.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Yahouza Sadissou Madobi