1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Burkina Faso: Adalci ga marigayi Thomas Sankara

October 11, 2021

A Burkina Faso an fara shari'ar kisan gillar da aka yi wa tsohon shugaban kasa Thomas Sankara shekaru 34 da suka gabata, a Ouagadougou babban birnin kasar.

https://p.dw.com/p/41XpH
Burkina Faso |  Prozess Thomas Sankara | 
Hoto: Katrin Gänsler/DW

Zaman kotun da ya kasance na farko, na gudana ne ba tare da halartar tsohon shugaban kasar da aka tilastawa ajiye mulki a shekara ta 2014 Blaise Compaoré ba. Compaoré dai shi ne ya jagoranci kasar bayan yi wa Shugaba Sankara juyin mulki.

A ranar hudu ga watan Agustan shekara ta 1983, Sankara ya karbe madafun iko a Burkina Fason. Sai dai an halaka shi a ranar 15 ga watan Oktoba na shekara ta 1987, shekaru hudu bayan kama mulkin. Shekaru 34 bayan halaka shi, an fara gudanar da shari'a kan kisan gillar da aka yi masa. Mutane 12 cikin 14 da ake zargi da kisan nasa sun halarci zaman kotun na wannan Litinin din, ciki har da babban hafsan sojan kasar da ya jagoranci harbe-harben juyin mulkin janar Gilbert Diendéré mai shekaru 61 a duniya da ke zaman babban na hannun daman Blaise Compaoré. Da take nuna takaicinta kan rashin halartar tsohon hambararren shugaban kasar Burkina Fason, Compaoré, da ke kan gaba cikin wadanda ake zargi da kisan na Thomas Sankara mai dakin marigayin Maria Sankara cewa ta yi:

"Bai dace a ce bai halarci wannan zaman kotun ba, ya kamata ya samu kwarin gwiwar zuwa sauraren karar a gaban kotu, to amma kasan ba kowa ke da irin wannan kwarin gwiwar ba, hakan ya nuna cewa yana gujewa gaskiya."

Blaise Compaoré dai ya kwashe shekaru 27 yana mulki a Burkina Faso, kafin zanga-zangar adawa da gwamnatinsa ta tilasta masa ajiye mulki a shekara ta 2014 tare da tserewa makwabciyar kasa Ivory Coast ko Cote d'Ivoire, inda ya samu mafaka, kana a shekara ta 2016 suka ba shi shaidar zama dan kasa. Compaoré da lauyansa ya sanar tun a makon da ya gabata cewa ba zai halarci zaman kotun da ya kira da "shari'ar siyasa" ba, ya sha musanta zargin kitsa kisan na Sankara. A cewar lauyan nasa, shari'ar na cike da kura-kurai kuma har yanzu Compaoré na da rigar kariya a matsayinsa na tsohon shugaban kasa.

"Sankara ya kasance lu'ulu'unmu", inji Jean-Hubert Bazié
"Sankara ya kasance lu'ulu'unmu", inji Jean-Hubert BaziéHoto: Katrin Gänsler/DW

Har yanzu dai Sankara na zaman gwarzo a Burkina Faso, inda ma har suka gina mutum-mutuminsa. A yanzu haka dai, wajen da mutum-mutumin Sankaran yake, na zaman wuri da ya fi samun masu ziyara a kasar. Tsohon dan jarida Jean-Hubert Bazié na zaman mai magana da yawun cibiyar tunawa da Thomas Sankara ya nuna farin cikinsa da wannan shari'a yana mai fatan ganin gaskiya ta yi halinta.

"Duk da kasancewa karamar kasa mai al'umma kadan, tasirin Sankara na da matukar yawa. Mahaifin Sankara ya kwashe tsawon lokaci yana jiran Blaise Compaoré ya kai masa ziyara, domin sanin abin da ya faru da dansa. Sai dai har ya koma ga mahaliccinsa, Compaoré bai kai masa ziyarar ba."

A nasa jawabin Eric Ismael Kinda kakakin gamayyar kungiyoyi masu akidar siyasa ya nunar da cewa har yanzu Thomas Sankara na zaman gwarzon matasan Burkina Faso, wanda ya yaki rashin gaskiya da cin hanci da rashin adalci da rashin aikin yi da jahilci da kuma talaucin da ya fi shafar matasa. A cewarsa tun bayan kisansa ake ta kiraye-kirayen kan a tabbatar da gaskiya, kuma sun jima suna jiran ganin an gudanar da shari'ar. Ya kara da cewa ya so Compaoré ya halarci zaman shari'ar, inda ya ce ya ki halarta ne domin rashin gaskiya da kuma raina shari'a da ya kwashe tsawon shekaru 27 na mulkinsa yana yi.

Blaise Compaoré (hagu) na da bakin jini a idanun da yawa na al'umar Burkina Faso ba kamar Thomas Sankara ba
Blaise Compaoré (hagu) na da bakin jini a idanun da yawa na al'umar Burkina Faso ba kamar Thomas Sankara ba

Aziz Salmone Fall masanin harkokin siyasa kana jagoran gangamin neman yin adalci ga Thomas Sankara na kasa da kasa cewa ya yi:

"Mun kwashe shekaru 25 muna fafatawa kan lamarin Sankara. Mun shigar da kararraki da dama, mun yi rashin nasara a kotun koli. Mun garzaya zuwa Kwamitin Kare Hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya, wanda a shekara ta 2006, ya amince da karar da matarsa da 'ya'yansa suka shigar. Duk da barazana da matsaloli da muka fuskanta, mun ci gaba da aikinmu."

Salmone Fall ya ce, shi ma ba zai halarci zaman kotun ba har sai Compaoré ya halarta, duk da kwashe tsawon shekaru da ya yi yana jagorantar wannan fafutuka. An halaka tshohon shugaban Burkina Fason Thomas Sankara mai shekaru 37 a duniya tare da wasu na hannun damansa 12 a birnin Ouagadougou, yayin da suke tsaka da taro kan makomar kasar da ya sauyawa suna daga Upper Volta zuwa Burkina Faso.