1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara yakin neman zabe a kasar Masar

May 3, 2014

Janar Abdel Fatah al-Siisi da ke da goyon bayan sojoji da kuma Hamdine Sabbahi da 'yan adawa suka tsayar ne za su fafata a zaben shugaban kasa a Masar.

https://p.dw.com/p/1BtAm
Hoto: Ahmed Wael

A wannan asabar aka fara yakin neman zaben shugaban kasa da zai gudana a ranakun 26 da kuma 27 na watan Mayu a Masar. Tuni ake ta hasashen cewa tsohon hapsan hapsoshin sijojin kasar Abdel Fatah Al-Sissi ne zai lashe zaben.

Sai dai wannan yakin neman zaben zai gudana na ne a daidai lokacin da hare-haren bama-bamai suke yawaita a Masar tare kuma da muzguna 'yan kungiyar 'Yan Uwa Musulmi a wannan kasa. Masar ce dai kasar da tafi dukkanin kasashen yankin Larabawa yawan al'umma.

Zaben dai zai wakana ne watanni 11 bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatin shugaban kasar na farko da aka zaba ta hanyar demokaradiya Mohamed Morsi. Tun bayan tumbuke gwamnatinsa ne, jam'iyya mafi karfi a wannan kasa ta 'Yan Uwa Musulmi ke fuskantar takurawa ta ba sani ba sabo daga sabbin hukumomin kasar.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe