1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gaza gabatar da kasafin kuɗi na shekara na Najeriya

November 19, 2013

Rikicin siyasar da ta ke fama da shi ya sa a karo na biyu shugaba Goodluck Ebele Jonathan ya gaza gabatar da kasafin kuɗin na Naira Trilliyan huɗu da miliyan dubu ɗari bakwai da saba'in ga majalisun dokoki.

https://p.dw.com/p/1AKoi
Description en:House of Representatives of Nigeria Date 16 September 2005, 11:13 Source The House of Representatives Author Shiraz Chakera ou are free: to share – to copy, distribute and transmit the work to remix – to adapt the work Under the following conditions: attribution – You must attribute the work in the manner specified by the author or licensor (but not in any way that suggests that they endorse you or your use of the work). share alike – If you alter, transform, or build upon this work, you may distribute the resulting work only under the same or similar license to this one.
Majalisar dokokin NajeriyaHoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

Duk da cewar dai tun da sanyin safiya jami'an tsaron ƙasar suka mamaye ɗaukacin harabar majalisun, sannan kuma aka ce an yafe wa duk wani ƙaramin da matsakaicin ma'aikaci zuwa aikinsa a yau, ba'a kai ko'ina ba aka fara raɗe-raɗe na ƙarauce wa shugaban ƙasar da aka tsara zai baiyana domin miƙa kasafin kuɗin ƙasar . Kafin daga baya shugabannin majalisun biyu su karanta wata wasiƙar da shugaban ya miƙa da safiyar yau wadda kuma a cikinta ya ambato banbanci na ma'unin kasafin a tsakanin dalar Amirkla 76.50 da majalisar dattawan Nnajeriyar ta amince da kuma 79 da ke zaman matsayin 'yan uwansu wakilai. A matsayin hujjarsa ta ƙaurace wa zaman da ke zaman na al'ada a shekara.

Taƙaddama a kan kasafin tsakanin gwamnatin da majalisun

To sai dai kuma majiyoyi a cikin majalisun biyu dai na ambato jeri na dalilai kama daga ƙoƙari na tawaye ga shugaban ƙasar a ɓangren yayan sabuwar PDP da ke shirin maida martanin ga irin wannan bita da ƙuli da ake yi wa shugabaninsu wattanni kusan biyu da suka gabata. Ko bayan nan dai sai kuma tsoro na zanga-zangar ma'aikatan majalisar da ke bin wasu jeri na alawus-alawus da kuma suka lashi takobin fito na fito yayin kasafin.Hon Alhassan Ado Doguwa dai ɗan majalisar wakilan ƙasar ne a Kano kuma jigo a cikin ya'yan ƙungiyar ta sabuwar PDP. Ya ce: :''Ruɗani ko kuma banbanci na ƙididdigar kasafi dai sabon matsayin dai na zaman alamu na tasirin rikicin cikin gidan jam'iyyar PDP mai mulki ga harkokin ƙasar ta Najeriya. Rikicin kuma daga dukkan alamu ya kama hanyar Barazana ga makomar demokraɗiyyar ƙasar dai tai nisa a cikin tangal-tangal.

Treffen nigerianischer Gouverneure. Foto: DW-Korrespondent Ubale Musa, 26.6.2013 in Abuja
Shugaban Najeriya Gooluck Jonathan tare da wasu gwamnonin.Hoto: DW

Rikicin PDP na taka rawa wajen rashin fahimtar da ake samu a majalisar

Nasarar 'yan sabuwar PDP dai na nuna irin jan aikin da ke gaban al'ummar ƙasar da ta share tsawon lokaci tana jiran gani na sauya rayuwar da gwamnatin ta alƙawarta amma kuma ke neman ƙarewa a cikin ɓacin rai na siyasa irin na son zuciya da na isa. To sai dai kuma a faɗar Hon Aminu Suleiman:'' 'Yan majalisar ba su da ɓuri na tsaoratar da gwamantin da nufin murɗe wuya da ɗorata bisa hanyar cika ra'ayi da bukatunsu''.Kure ƙarfin mai ƙarfi ko kuma barazana ga tsari na demokraɗiyya dai, ra'ayi dai na banbanta can a majalisar dattawa game da matakin shugaban na ƙaurace wa ziyarar a tsakanin masu tunanin ya dace da kuma masu ganin matakin bai zo guda da tsari irin na shugabanci ba, a faɗar Senator Abudlkadir Alkali jajere. Da ke zaman ɗan majalisar dattawan ƙasar daga jihar Yobe wanda kuma ya ce ƙaurace wa shugaban ƙasar laifi ne babba.To sai dai kuma in har tsallen murna na ga zuciyoyin ya'yan na sabuwar PDP dai daga dukkan alamu har yanzu akwai sauran tafiya a tsakanin su da ɓuri tabbatar da tsoratar da shugaban a faɗar Ahmed Ali Gulak da ke zaman mashawarcin shugaban ƙasar.

PRESIDENT GOODLUCK JONATHAN (3RD L) ; VICE-PRESIDENT NAMADI SAMBO (4TH L) WITH MEMBERS OF THE COMMITTEE ON PROLIFERATION OF SMALL ARMS AND LIGHT WEAPONS AFTER THEIR INAUGURATION AT THE PRESIDENTIAL VILLA ABUJA ON WEDNESDAY (24/4/13).
Gooluck Jonathan tare da wasu masu faɗa a ji a Najeriya.Hoto: DW/A. Ubale Musa

Daga ƙasa za a iya sauraron wanan rahoto hade da hira da Garzali Yakubu ya yi da Farfesa Garba Ibrahim masanni kan tattalin arziki daga Najeriya.

Mawallafi : Ubale Musa
Edita : Abdourahamane Hassane

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani