An hallaka masu aikin rigakafin chutar shan inna a Najeriya
February 8, 2013Talla
Wasu 'yan bindiga sun hallaka kimanin mutane tara masu aikin rigakafin chutar shan inna, a garin Kano na arewacin Tarayyar Najeriya.
Mazauna garin da 'yan sanda sun ce lamarin ya faru cikin hare hare guda biyu, a wasu cibiyoyin kula da alluran rigakafin chutar ta shan-inna wadanda ke birnin. Daga bisani maharan sun tsere.
Najeriya tana cikin kasashe uku na duniya da suka rage dauke da chutar, sun hada da Afghanistan da Pakistan.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Usman Shehu Usman