1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An haramta barar almajirai a Senegal

Gazali Abdou TasawaJuly 6, 2016

Shugaban Senegal Macky Sall ya bada umarnin haramta barace-barace da dubunnan almajirai ke yi a saman titunan kasar.

https://p.dw.com/p/1JKnL
Die Bettel-Schüler aus Nordnigeria
Hoto: DW

Shugaba Macky Sall ya sanar da wannan mataki ne a lokacin wata hira da ya yi da manema labarai jim kadan bayan kammala Sallar idi karama da kasar ta sallata a wannan Laraba inda ya ce ya bai wa gwamnatinsa umarni kan ta dauki duk matakan da suka dace domin kawo karshen wannan tabi'ar ta ci da gumin yara marasa galihu da wasu mutane ke yi da sunan addinin Muslunci a kasar ta Senegal.

Wasu alkalumman bincike na gwamnatin kasar ta Senegal na shekara ta 2014 sun nunar da cewa almajirai kimanin dubu 30 ne akasarinsu 'yan asalin kasashe makobta ke yawon bara a birnin Dakar kadai a ko wace rana ta Allah sanye da tsumma kuma ba takalmi.