1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An haramtawa Nawaz Sharif yin takara

Zainab MohammedDecember 3, 2007
https://p.dw.com/p/CWHR

Hukumar zabe Paskistan ta haramta tsohon prime minisatan kasar kuma shugaban Adawa Nawaz Sharif,daga yin takara a zaben kasa baki daya da zaa gudanar a ranar 8 ga watan janairu.Hukumomin kasar ta pakisantan dai sun bayyana hukuncin da aka yiwa Sharrif a shekara ta 2000,da kasancewa dalilan da suka sa aka ki karban takardun sa na shiga takara.Laifin Sharif wancan lokacin dai ya hadar da dakatar jirgin dake dauke da hafsan soji na wancan lokacin Pervez Musharrif,daga sauka a Pakistan a watan oktoban 1999.Sakamakon hakan ne Musharraf da sojojin Kasar suka hambare gwamnatin Nawaz Sharif..Yau ne dai Sharif ya isa birnin Islamabad ,domin tattaunawa da sauran shugabannin jamiiyyun adawa da suka hadar da tshohuwar premmier Benezir Bhutto,adangane da shirinsu na kauracewa zaben na janairu.