An kafa bankin BRICS
July 16, 2014A kasar Brazil shugabannin kasashen da tattalin arzikinsu ke habaka cikin sauri da aka sani da Brics, sun kaddamar da wani banki da kudi dalar Amirka biliyan 100, wanda za su rika yin amfani da su don taimakawa wata kasa da ta fiskanci talaucewa. Wannan dai shi ne matakin farko mafi girma da suka dauka, wajen tabbatar da sun kafa wata hukumar kudi da za ta yi gogayya da Bankin duniya da Asusun bada lamuni na IMF, wanda kasashen Yamma ke juya akalarsa. Za a kafa bankin a birnin Shanghai na kasar China, kana kasar Indiya za ta fara shugabantar bankin na shekaru biyar, kafin daga bisani Brazil ta karba sai kuma Rasha ta bi. Kungiyar da ke karkashin kasashen Brazil, Indiya, Rasha, China da Afirka ta kudu, taron nasu yana samun halartan dukkan shugabannin biyar.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu