1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kafa dokar hana fita a jihar Yobe a Najeriya

October 22, 2012

A ƙoƙarin da ake yi na sake dawo da zaman lafiya bayan tashin hankalin da ya auku a Potiskum, hukumomi a jihar Yobe sun kafa dokar hana yawo a garin.

https://p.dw.com/p/16UjO
Soldier patrol to monitor protesters at Ojota district in Lagos on January 16, 2012. Nigerian security forces fired tear gas and shot into the air Monday to disperse around 300 protesters in Lagos as authorities moved to prevent demonstrations in various parts of the country. Nigerian unions announced on January 16 they were suspending a week-old nationwide strike over fuel prices which has shut down Africa's most populous nation and brought tens of thousands out in protest. AFP PHOTO/PIUS UTOMI EKPEI (Photo credit should read PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images)
Nigeria Sicherheitskräfte SoldatenHoto: Getty Images/AFP

Gwamnatin jihar Yobe da ke a yankin arewa maso gabashin Tarayyar Najeriya ta kafa dokar hana yawo a garin Potiskum mai nisan kilomita ɗari daga Damaturu fadar gwamnatin jihar, daga ƙarfe huɗu zuwa karfe bakwai na safe, domin shawo kan matsalar tsaro da ke addabar garin a ‘yan kwanakin nan. Wata sanarwa da gwamnatin ta fitar ta bayyana cewa ta ɗauki wannan mataki ne bayan wani taro da aka gudanar da masu kula da tsaro domin kawo ƙarshe hasarar rayuka da dukiyoyi da ake yi a garin sanadiyyar tashin hankali da hare-hare da ake kaiwa. Sanarwar ta kuma bukaci da kowa ya zauna gida a dai-dai lokacin da wannan doka ta fara aiki ,tare da neman jama'a su taimaka wa jami'an tsaro a ayyukan su na wanzar da zaman lafiya.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasir Awal