1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kafa dokar ta-ɓaci a faɗin ƙasar Masar

Usman ShehuAugust 14, 2013

An hallaka mutane da dama a ci-gaba da matakan amfani da ƙarfi, don tarwasta magoya bayan Mursi,

https://p.dw.com/p/19Q2B
Riot police gather during clashes with members of the Muslim Brotherhood and supporters of deposed Egyptian President Mohamed Mursi, around Cairo University and Nahdet Misr Square, where they are camping in Giza, south of Cairo August 14, 2013. Egyptian security forces killed at least 30 people on Wednesday when they cleared a camp of Cairo protesters who were demanding the reinstatement of Mursi, his Muslim Brotherhood movement said. REUTERS/Mohamed Abd El Ghany (EGYPT - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)
Jami'an tsaron Masar a filin dagaHoto: Reuters

Ƙashen duniya sun yi Allah wadai da matakin yin amfani da ƙarfi wanda sojan ƙasar Masar suka yi, don tarwatsa magoya bayan Muhammad Mursi. Firaministan ƙasar Turkiya Raccip Tayyip Erdogan, ya yi ƙira ga ƙasa da ƙasa, lallai su dau mataki kan mahuntan ƙasar ta masar, wadanda suka fara yin amfani da ƙarfi kan sansanin mutanen da basa ɗauke wani makami. Kawo yanzu dai ƙasashen Birtaniya, Jamus da Faransa na daga cikin wadanda suka yi Allah wadai da mataki, inda ita su kuwa ƙasashen Iran da Qatar suka yi kakkausar suka bisa matakin sojojin na Masar. Sakatare janar na MDD Ban Ki-moon, ya bukaci da hukumomin jami'an tsaron Masar dai bayan matakin da suka dauka, aƙalla mutane 124 suka mutu, wasu da dama suka jikkata, yayinda kuma aka tsari wani ƙusa a kungiyar yan uwa musulmai, ta Muslim Brotherhoods. An kuma kafa dokar ta ɓaci na tsawon wata guda a fadin ƙasar, abinda ke nuna cewa an haramta duk wata zanga-zanga.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu

RTR