1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kafa sabuwar gwamnati a Masar

July 16, 2013

Gwamnatin wadda ke da manbobi kusan guda 30 galibinsu masu adawa ne da tsohuwar gwamnatin Mursi da kuma Hosni Mubarak.

https://p.dw.com/p/199Ip
This image released by the Egyptian Presidency on Tuesday, July 16, 2013 shows interim President Adly Mansour, center, with his new cabinet ministers at the presidential palace in Cairo, Egypt. Egypt's interim president has sworn in a new Cabinet, the first since the ouster of the Islamist president by the military nearly two weeks ago. The new government, sworn in Tuesday, is led by Prime Minister Hazem el-Beblawi, an economist, and features the promotion of Defence Minister Gen. Abdel-Fattah el-Sissi, who ousted Mohammed Morsi on July 3, to deputy prime minister. He also retains the defence portfolio. (AP Photo/Egyptian Presidency)
Hoto: picture-alliance/AP Photo

An naɗa sabuwar gwamnatin ne wadda aka ƙaddamar da bikin rantsar da sabbin manbobinta a gaban shugaban gwamnatin wucin gadi Adly Mansur da fira mistan Hazam Belblawi; da kuma sauran shugabannin sojin da suka kifar da gwamnatin Muhammad Mursi.

Matsayin ministan tsaro ya tsaya ga janar Abdel Fatah Al-Sisi mutumin da shi ne ƙusa a juyin mulkin da aka yi a farkon wannan wata  wanda kuma aka naɗa shi muƙadashin shugaban gwamnatin. Yayin da Nabil Fahmy tsohon jakadin ƙasar a Amirka ya zama minsitan harkokin waje, kana na kuɗi aka miƙa shi ga wani msanin tattalin arziki da ke a  Bankin Duniya Ahmad Galal. A karon farko an naɗa mata guda uku a cikin sabuwar gwamnatin.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita       : Zainab Mohammed Abubakar