1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane shida sun mutu a harin cibiyar G5 Sahel a Mali

Gazali Abdou Tasawa
June 29, 2018

Wani hari da aka kai a wannan Juma'a a hedikwatar rindunar kawancan G5 Sahel da ke a tsakiyar kasar Mali ya yi sanadiyyar mutuwar mutane shida kana wasu da dama suka jikkata. 

https://p.dw.com/p/30Zdj
Mali Angriff auf G5 Sahel Basis in der Stadt Sevare
Hoto: Getty Images/AFP

Wata majiyar tsaro kaar ta Mali ta ce wani dan kunar bakin wake ne ya soma tayar da jigidar bama-baman da ke a jikinsa a lokacin da sojoji suka yi kokarin hana masa shiga cikin barikin sojan kafin daga bisani sauran maharan su buda wuta kan sojojin ta G5 Sahel da ke a garin Sevare na tsakiyar kasar ta Mali. 

Sai dai rahotanni na cewa ya zuwa yanzu kura ta lufa sai dai an kawo daukin karin sojoji a birnin. Wannan shi ne karo na farko da aka hari hedikwatar rindunar ta G5 Sahel da ta hada kasashen Mali, Burkina Faso, Nijar, Moritaniya, da Tchadi da nufin kawar da kungiyoyin 'yan ta'adda daga yankin na Sahel.