1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai wa 'yan gudun hijira hari a Darfur

Gazali Abdou Tasawa
May 24, 2018

MDD ta ce fararen hula da dama ne suka halaka wasunsu kuma suka ji rauni a cikin wasu jerin hare-hare da aka kai a sansanin 'yan gudun hijira na yankin Darfur a wannan mako. 

https://p.dw.com/p/2yHb6
Kamerun Zentralafrikanische Republik Flüchtlinge in Kousseri
Hoto: AP

Rundunar kawancan sojojin MDD da da na Kungiyar Tarayyar Afirka wato Muniad wacce ta sanar da wannan labari a wannan Alhamis ba tare da bayar da alkalumma na adadin mutanen da suka mutu ko suka ji rauni ba, ta ce an kai hare-haren ne tsakanin 21 zuwa 23 ga wannan wata na Mayu a sansanonin 'yan gudun hijira na Khamsa Dagaig da na Ardayba da kuma na Jedda wadanda ke kunshe da dubunnan 'yan gudun hijira na yankin Tsakiyar Darfur. 

'Yan gudun hijirar dai sun dora alhakin kai wannan hari ga kungiyar RSF ta wasu mayakan sa kai na kasar ta Sudan da ke goyon bayan gwamnati.