1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kama bakin haure a Jihar Bayelsa

July 14, 2014

Rashin tsaro da Tarayyar Najeriya ke fuskanta ya janyo kame-kamen bakin haure a yankin kudancin kasar

https://p.dw.com/p/1CcqA
Hoto: picture-alliance/dpa

Tun da sanyin safiyar wannan Litinin gamayyar jami'an tsaro a birnin Yenagoa na Jahar Bayelsa da suka hada da 'yan sanda da soji da jami'an hukumar kula da shige da fice suka gudanar da wani aikin kama baki 'yan kasashen ketare da ke zaune a jihar ba bisa kaida ba. Sai dai kuma Kamen an yi shi ne na kan mai uwa da wabi, inda hukumar kula da shige da fice a jihar ta ce, za ta tantance daga baya.

Wannan aikin kamen da jami'an tsaro a Jihar ta Bayelsa suka gudanar, akwai al'ummar arewacin Najeriya da dama da lamarin ya ratsa da su, bayan baki 'yan Kasashen ketare da hukumar shige da fice ta kasa ta ce, su take nufin kamawa, musamman wadanda ba su da takardun zama a Najeriya.

Nigeria Soldaten
Hoto: AFP/Getty Images

Wannan yanayi da ya jefa 'yan arewacin Najeriya da baki cikin kaduwa matika ganin cewar, wannan aiki bai gudana da rana ba. Shugaban hukumar shige da fice da ke Jahar ta Bayelsa Gambo Abdu Wiyap ya ce tilas ne a rika daukan matakan kariya.

Mawallafi: Muhammad Bello
Edita: Suleiman Babayo