1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kamalla zaben 'yan majalisa a Mali

November 24, 2013

'Yan Malin da suka fito kada kuri'a don zaben 'yan majalisa ba su kai na zaben shugaban kasa ba. Sai dai an harbi masu zabe a Kidal inda mutane uku suka jikata.

https://p.dw.com/p/1ANL6
Mali's president Ibrahim Boubacar Keita casts his vote at a polling station in Bamako, on November 24, 2013. Malians voted on November 24 in parliamentary elections intended to cap the troubled west African nation's return to democracy but overshadowed by the threat of Islamist reprisals. AFP PHOTO / HABIBOU KOUYATE (Photo credit should read HABIBOU KOUYATE/AFP/Getty Images)
Hoto: Habibou Kouyate/AFP/Getty Images

Al'ummar kasar Mali sun kammala kada kuri'a a zaben 'yan majalisun dokoki cikin tsauraran matakan tsaro bisa fargabar 'yan tawaye ka iya kai hare-hare da ka iya kawo cikas ko kuma nakasu ga zaben. Sai dai rahotanni sun bayyana cewa mutanen da suka fito domin kada kuri'unsu sun gaza wadanda suka fito yayin zaben shugaban kasa da aka gudanar cikin watan Agustan da ya gabata.

Rahotanni sun bayyan cewa a kalla mutane uku ne suka jikkata a yankin Kidal dake fama da rikici, sakamakon jifan masu kada kuri'a da duwatsu da magoya bayan jam'iyyar dake fafutukar samar da 'yancin kan yankin Azawad ta 'yan kabilar Abzinawa suka yi.Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya sun dauki matakan kare afkuwar rikici.

Kuri'un da aka kada dai na zaman mataki na karshe na dawo da gwamnatin da tsarin mulkin kasar ya amince da ita, biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar a cikin watan Maris na shekara ta 2012. Wannan dai ya haddasa fargabar cewa 'yan tawaye kan iya kwace iko da kasar baki daya. Saboda haka ne Faransa ta kaddamar da hare-haren soji a watan janairun da ya gabata domin dakile kokarin da masu kaifin kishin addini dake da alaka da alka'ida keyi na kwace iko da arewacin kasar.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe