1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kammalla taron Viena game da addinin musulunci

November 16, 2005
https://p.dw.com/p/BvKp

A birnin Vienna na kasar Ostriyya, an kamala zaman taro yini 3, a game da addinin musulunci.

Mahalarta taron da su ka hada da shugaban kasar Afganistan Hamid Karzai, da na Iraki Jallal Talabani, da tsofan shugaban kasar Iran, Muhamed Khatami, da sauran massana, ta fannin addinin musulunci, sun yi masanyar ra´ayoyi, a game da mattakan tabbatar da zaman lahia, a dunia ta hanyar anfani da dokokin addinin musulunci.

Gwamnatin kasar Ostriyya, ta dauki dauniyar gayyatar wannan haduwa, a shirye shiryen da ta ke, na karbar shugabancin kungiyar gammaya turai, ranar 1 ga watan janairu mai zuwa.

Kasancewar dimbin ra´ayoyi, da banbance da a ka samu, ba a cimma nasara fiddo da sanarwar hadin gwiwa ba, a karshen taron, amma wannan ba ya nufin cewa, taron ya waste baran baran, iinji kakakin wandan su ka tsara shi.

Saidai baki daya, sun cimma daidaito a kan wajibcin yaki da ta´adanci, wanda kwata kwata ya sabawa dokokin addinin musulunci.