An kashe Bajamushe daya a Sagamu na Ogun
October 27, 2014Talla
Masu aiko da rahotanni suka ce 'yan bindigar sun bude wuta ne kan motocin da Jamsuwan ke ciki, wanda suke yi wa kamfanin nan na Julius Berger aiki a kasar a ranar Jumma'ar da ta gabata kamar yadda mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar ta Ogun ta shaida wa manema labarai.
Mai magana da yawun kamfanin na Julius Berger a Najeriya ya tabbatar da wannan labarin kuma ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta bayyana cewar ita ce ke da alhakin kisan Bajamushe da kuma sace abokin aikinsa.
Kame 'yan kasashen waje da nufin neman kudin fansa abu ne da ke zaman Jampa a Jos a kudancin tarayyar ta Najeriya.