An kashe jagoran addini a Bangladesh
April 11, 2015Talla
Muhhamad dan shekaru 63 jagoran jam'iyyar 'yan adawa ta masu kishin addini,wata kotun ta musammun da aka girka ta sameshi da hannu a kisan ƙare dangi da aka aiwatar a lokacin yaƙin samun yanci kai na ƙasar daga Pakistan a shekarun 1971.
Tun da farko kotun ƙollin ƙasar ta yi watsi da ƙaran da ya ɗaukaka a kan hukuncin kisan.