1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe mutane a cikin wata zanga zanga a Iraki

April 23, 2013

Mutane a ƙalla guda 27 suka gamu da ajalinsu yayin da wasu 70 suka samu raunika a garin Houweijah da ke a yammancin Iraki.

https://p.dw.com/p/18LQ6
A man is brought to a hospital on a stretcher after after being wounded in a clash between Iraqi forces and Sunni Muslim protesters in Kirkuk, 250 km (155 miles) north of Baghdad April 23, 2013. At least 26 people were killed when Iraqi security forces stormed a Sunni Muslim anti-government protest camp near Kirkuk on Tuesday, starting a gun battle between troops and protesters, local officials and military sources said. REUTERS/Ako Rasheed (IRAQ - Tags: CIVIL UNREST POLITICS)
3Hoto: Reuters

An dai sha artabu ne tsakanin jama'ar yan sunni masu yin addawa da gwamnatin fira minista Nuri Al Maliki, da kuma jami'an kwantar da tarzoma a arewacin birnin Bagadaza.

Jami'an tsaron dai sun afkawa wani gungun masu yin gangamin a garin Houweijah da ke a yammancin birnin Kirkouk, da ke yin wata zanga zanga tun makonni da dama da suka wuce inda suka buɗe masu wuta. Ofishin ministan cikin gida na ƙasar ya ce sojojin sun kai harin ne, bayan da wa'adin da gwamnatin ta giciyawa yan sunni na su miƙa wanda ya kashe wani soji gwamnatin a yankin a makon jiya ya kawo ƙarshe.Tun a tsakiyar watan Disamba da ya gabata yan ɗarikar Sunni ke ta gudanar da jerin zanga zanga a yankin arewaci na kasar, domin matsa ƙaimi ga shugaban gwamnatin da ya yi marabus.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman