1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe mutane da dama a birnin Bangui

Walton, LuciaDecember 27, 2013

Ƙungiyar agaji ta Red Cross ta ce ta tsintsi gawarwakin mutane guda 40 a kan tittunan Bangui babban birnin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

https://p.dw.com/p/1AhIS
Zentralafrika Unruhe Protest am 23.12.2013
Hoto: MIGUEL MEDINA/AFP/Getty Images

Wani kakakin ƙungiyar daga Jeniva David Pierre Marquet ya ce yawanci waɗanda lamarin ya rutsa da su an yi amfani da makaman gargajiya wajen kashe su,sannan ya yi gargaɗin cewar addadin waɗanda suka mutu zai iya ƙaruwa saboda a halin da ake ciki a kwai unguwanin da jami'an agaji ba zasu iya kutsa kai.

 Ɗarurruwan mutane  dai na ta tserwa daga  birnin Bangui tun jiya,lokacin da sojojin sa kai kirista suka kashe sojoji Chadi guda shida waɗanda suke zargi da goyon bayan 'yan ƙungiyar SELEKA musulumi.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane

Edita        : Umaru Aliyu