1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe sojojin MDD a Mali

November 24, 2017

Sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da na Mali sun mutu sakamakon wani harin da 'yan bindiga su kai masu wani yankin kasar Mali.

https://p.dw.com/p/2oE2z
Mali UN Mission MINUSMA
Hoto: Getty Images/A. Kerner

Akalla sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD da na gwamnatin kasa Mali uku ne aka tabbatar da mutuwarsu a yau, sakamakon wani harin da 'yan bindiga su kai masu a wani yanki da ake kira Menaka.

Sanarwar da rundunar MINUSMA ta fitar, na cewa sun gamu da ajalinsu ne awasu jerin hare-haren yayin da suke sintiri a yankin na Menaka. Bayanai sun kuma ce su ma 'yan bindigar, da dama daga cikinsu sun halaka tare da jikkatar gwammai.

Ba a dai bayyana ko sojojin kiyaye zaman lafiyar daga wasu kasashe ne abin ya shafa ba, sai dai dama akwai sojojin kasashen Najeriya da kuma Togo da ke cikin rundunar. Ko cikin watan jiya ma dai an halaka sojojin Chadi akalla hudu da ke cikin wannan runduna.