1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe 'yan Boko Haram 300 inji sojin Najeriya

February 18, 2015

Kakakin rundunar sojin Najeriya Chris Olukolade ya ce an kashe masu ta da kayar bayan ne a yakin kwace garin Monguno kuma an kwace makamai masu tarin yawa.

https://p.dw.com/p/1Edkx
Nigeria Maiduguri Boko Haram
Hoto: picture-alliance/dpa

Sojojin Najeriya sun yi ikirarin kashe mayakan Boko Haram 300 a fafatawar da suka yi da masu ta da kayar bayan wajen sake kwace garin Monguno da ke jihar Borno ta arewa maso gabashin Najeriya. Kakakin rundunar sojin Najeriya Chris Olukolade ya ba da wannan sanarwa, inda ya kara da cewa an kwace makamai masu tarin yawa ko kuma an lalata su. Kawo yanzu ba wata kafa mai zaman kanta da tabbatar da wannan labari. Sojojin Najeriya hade da takwarorinsu na kasashe makwabta daga Chadi da Nijar da kuma Kamaru suna yakar 'yan Boko Haram da suka addabi yankin arewa maso gabashin Najeriya suna kuma kai hare-hare kan iyakokin kasar da kasashe makwabta.

Sai dai rahotanni daga karamar Hukumar Hong da ke arewacin jihar Adamawa na cewa yanzu haka ana zaman zullumi sakamakon harin da Boko Haram ta kai a kauye Gaya-Faya inda suka kona garin kurmus da hallaka mutane sama da talatin.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu