1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin zaben jihar Ekiti

July 16, 2018

Fadar gwamnatin Najeriya ta ce nasarar da APC ta samu a zaben jihar, alamar jin kunya ce ga tsohon gwamnan Ayodele Fayose da tsohon Shugaban Najeriyar Cif Olusegun Obasanjo.

https://p.dw.com/p/31X1E
Nigeria wählt Gouverneure und Regionalparlamente
Hoto: Reuters/Penney

Jagoran jam'iyyar APC ta kasa Ahmed Bola Tinubu ya ce batun tsohon Gwamna Fayose ya zama tarihi, yanzu an bude sabon babin ci gaba da yi wa jama'ar jihar Ekiti ayyukan Alhairi. Dr. Olusola Ayande dan jamiyyar APC ne a jihar Oyo, ya ce nasarar APC alama ce ta nasara a zabubbukan da za su biyo baya a Najeriya.

Nigeria Symbolbild Korruption
Ana zargi 'yan siyasan Najeriya da rabawa masu zabeHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Dr. Kayode Fayemi na jam'iyyar APC ya doke dan takarar jam'iyyar PDP da yawan kuri'u kuma gwamnan jihar kamin zaben Ayodele Fayose, sai dai jama'a sun koka da yadda zaben ke cike da zargin amfani da kudi a rumfunan zabe. Easther Nba shugabar wata kungiyar jaddada mulki ne da dimukuradiyya a Najeriya ta ce: "Siyasar Najeriya na cike da amfani da kudi ta inda jamma'a ba su da zabi illa subi yarima su sha kida, kuma hakan hanya ce ta neman raba kan al'umma."

Amma Mr. Oguntuase Mathias dan jami'yyar PDP ne da ke ganin dole a yi maganin amfani da kudi ta hanyoyi da dama a harkokin zaben Najeriya inda ya ce: " Kalubale ne ga shugabanni wajen amfani da hukumar wayar da kan jamma'a nuna illar amfani da kudi wajen zabe, ta haka ne kawai za a cimma manufa."

Alh. Muhammed Musa mazaunin jihar Lagos na ganin jami'iyyar APC a matsayin zakaran gwajin dafi a Najeriya, " Ina tabbatar da cewa nasarar zaben jihar Ekiti alama ce da ke nuna duk da makiya sun rufe jam'iyyar, amma Allah na cigaba da haskaka ta kuma haka za a yi a zaben shekarar 2019." a cewarsa.

Blickschutz für geheime Wahl in Nigeria
Yayin gudanar da zabubbuka a NajeriyaHoto: DW/Uwaisu A. Idris

Gwamnan jihar Kebbi Alh. Bagudu da ya zanta da wakilin DW Mansur Bala Bello a Ado Ekiti babban birnin jihar, ya ce "A yanzu haka alama ce da ke nuna jam'iyyar APC ta karbu a duk fadin Najeriya, kuma muna alfahari da haka." Masana ilmin siyasa da masu sharhi na da ra'ayin cewa sai an kawar da kalubale da ke tattare da siyasar Najeriya, idan har ana fatan cimma nasara a zabubbuka masu zuwa.