1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kulla yarjejeniya a tsakanin China da Sudan

February 2, 2007
https://p.dw.com/p/BuSY

Shugaban kasar Sin Hu Jintao, yace kasar Sin zata tallafawa kasar Sudan, wajen shawo kann rikicin yankin Darfur ta hanyar ruwan sanyi.

Wannan sanarwar tazo ne a dai dai lokacin da shugaban na Sin ke ziyarar aiki a kasar ta Sudan, aci gaba da ziyarar da yake ta kwanaki 8 a nahiyar Africa.

Bugu da kari shugaba Hu Jintao da Omar Al Bashir na Sudan sun rattaba hannu akan yarjejeniya ta fannin sadarwa da makamashi da kuma gine gine na rasa kasa.

Wannan ziyara dai ta Hu Jintao, tazo ne a dai dai lokacin da kasar ta Sin ke kara fuskantar matsin lamba na yin amfani da damar da take da ita, wajen tursasawa Sudan yarda da zuwan dakarun sojin Mdd izuwa yankin darfur.

Kasar dai ta China a yanzu haka na sayen kashi 60 na man da kasar ta Sudan take hakowa, ban da wata katafariyar cibiyar samar da wutar lantarki da take gina mata a kogin Nil.