1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rantsar da Firaministan kasar Masar

June 17, 2014

Shugaban gwamnatin kasar Masar Ibrahim Mehleb, tare da ministocinsa, sunyi rantsuwar kama aiki a wani mataki na fuskantar kalubanen dake gabansu.

https://p.dw.com/p/1CJcO
Ibrahim Mehleb Ägypten porträt 2014
Hoto: Reuters

Hakan ya wakana ne a wani buki na musamman da aka shirya, wanda shugaban kasar ta Masar Abdel Fattah Al-Sissi ya halarta, sannan a daidai wannan lokaci, aka ci gaba da rantsar da membobin majalisar gwamnatin da aka zaba a ranar Litinin.

Akasarin ministocin na wannan sabuwar gwamnatin, sun kasance tun na tsofuwar gwamnatin rikon kwarya ne suka sake dawowa, da suka hada da ministan tsaron kasar da na cikin gida, da ministan tattalin arziki, da na fasali, da na man fetur, da na wutar lantarki, sannan da ministan sadarwa dukkanni su, na tsofuwar gwamnatin ta rikon kwarya ce. Ana ganin mayar su wadannan tsofin ministocin, zai baiwa shugaban Al-sissi damar aiwatar da ayukan da ya sa ma gaba cikin gaggawa tare da sabuwar gwamnatin mai wakilai 31 a cikinta.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu