An rantsar da saban shugaban ƙasar Nigeria
May 29, 2007A Tarraya Nigeria an rantsar da saban shugaban ƙasa El-Haji Umaru Musa yar Aduwa, wanda yau a hukunce, ya gaji tsofan shugaban Olesegun Obasanjo.
Idandai ba amanta ba, hukumar zabe mai zaman kanta a Nigeria, ta bayyana Yar Aduwa, a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na ranar 21 ga watan Aprul, tare da ƙuri´u kussan milion 25, a yayin da mai bi masa,wato Jannar Muhamadu Buhari mai ritaya, ya samu ƙuri´u milion kussan 7.
Bayan shugaban ƙasar kotin ƙoli ta rantsar da mataimakin sa, Goodluck Jonathan, tsofan gwamna jihar Bayelsa.
Sannan a jihohi daban-daban, an rantsar da sabin gwamnoni.
A lokacin bikin rantsuwar, Umaru Musa Yar Aduwa,mai shekaru 55 a dunia, ya rantse da Alƙur´ani mai tsarki , tare alƙawarta gudanar da aiki daidai yadda kundin tsarin mulkin ƙasa ya tanada.