1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rufe oifisoshin jakadancin Amirka a Gabas ta Tsakiya

August 2, 2013

Amirka ta rufe ofisoshin jakadancinta da ke wasu kasashe na yankin Gabas ta Tsakiya domin tsoron hare-haren da mai yiwuwa ne ofisoshin su fuskanta.

https://p.dw.com/p/19J7J
Ausschnitt: (FILES) -- File picture dated June 29, 2004 shows a private security guard standing at the front entrance of the new US Embassy building in in Baghdad's Green Zone. The United States inaugurated its gigantic new embassy in Baghdad on January 5, 2008, ushering in what American officials described as a new era in relations with Iraq nearly six years after it invaded the country. Officials moved into the new 700-million dollar embassy weeks ago but celebrated its opening today, four days after the United States officially handed over to Iraq security control of the Green Zone. AFP PHOTO/POOL/SCOTT NELSON/FILES (Photo credit should read SCOTT NELSON/AFP/Getty Images)
Hoto: Scott Nelson/AFP/GettyImages

Gwamnatin Amirka ta ce wannan wani mataki ne da aka dauka bisa dalilai na tsaro. Gidan telebijan CBS ya ba da rahoton da ke nuna cewa an samu labarun da ke nuni da cewa kungiyar Alka'ida na shirin kai hare-hare. Hakan kuma na da nasaba da sukan da kungiyar 'Yan uwa Musulmi ke wa sakataren harkokin wajen Amirka, John Kerry, wanda ya kira juyin mukin da sojoji suka yi wa Shugaba Mohammed Mursi tamkar sake girka demokradiya. Wani mai magana da yawon kungiyar 'Yan uwa Musulmi ya ce gwamnatin Amirka na da hannu a juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar ta Masar, inda har yanzu ake ci gaba da samun rudani. Su dai magoya bayan Mursi sun yi kira da a ci gaba da zanga-zanga.

Ministan harkokin wajen Jamus, Guido Westerwelle a yayin ziyarar da ya kai a Masar ya yi gargadi game da kara dagulewar tashin hankali.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammad Nasiru Awal