1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rusa majalisar dokokin Italiya

Ramatu Garba Baba
December 28, 2017

Shugaban kasar Italiya Sergio Mattarella ya sanar da rusa majalisar dokokin kasar a gabanin gudanar da babban zaben kasar na watan Maris na shekara 2018.

https://p.dw.com/p/2q4bX
Italien Präsident Sergio Mattarella löst Parlament auf
Hoto: Reuters/Presidential Press Office

Firaiministan kasar Italiya Paolo Gentiloni ya baiyana takaici kan yadda gwamnatin kasar ta gagara aiwatar da dokar da za ta bai wa yaran da iyayensu suka kasance bakin haure shedar zama 'yan kasa. Batun ko za a bai wa wadannan yara da suka kai dubu dari takwas da aka haifa ko aka shigo kasar ta Italiya tun suna 'yan yara shedar zama 'yan kasa ya soma mamaye kamfain na zaben kasar mai karatowa. Sai dai kuma rarrabuwar kannun da aka samu a tsakanin 'ya'yan jam'iyya mai mulki dama na adawa ya sa ba a iya cimma wannan manufa ba.

Jam'iyyar Demokratik mai mulki ta gagara samun kuri'un 'yan majalisun da ake bukata duk kuwa da fatan Firaiministan na ganin an yi hakan. Tururuwan 'yan gudun hijra  daga wasu kasashen Afrika zuwa Turai, musanman 'yan gudun hijrar da suka fito daga kasashen da ake fama da rikice rikice ko yunwa a shekarun baya bayan nan ya rarraba kan masu zabe a kasashen Turai bisa damuwa na rashin tsaro da ake samu a kasashen da aka bai wa wadannan mutanen mafaka.