1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sake kama wani da hannu a hare-haren Faransa

Suleiman BabayoDecember 24, 2015

An tuhumi mutum na tara a Belgiyam bisa hannu a hare-haren birnin Paris na Faransa cikin watan Nuwamba da mutane 130 suka hallaka.

https://p.dw.com/p/1HTPB
Belgien Brussels Polizei Anti Terror Polizisten
Hoto: Reuters/B. Tessier

Mahukuntan kasar Belgium sun kama mutum na tara da ake zargi da hannu kan hare-haren da aka kai birnin Paris na Faransa da suka yi sanadiyar hallaka mutane 130, a watan jiya na Nuwamba. Masu gabatar da kara sun ce wanda ake tuhumar dan shekaru 30 da haihuwa yana da danganta da maharan.

Mahukuntan sun ce wanda aka kama sunansa Abdoullah C kuma yana takardun dan-kasa na Belgium. Tuni masu bincike suka ba da umurnin ci gaba da tsare shi bisa zargin hannu wajen aiwatar da ta'addanci.