1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sake roko da a kara yawan taimako ga Pakistan

October 25, 2005
https://p.dw.com/p/BvNt
Jami´an ba da agaji na kasa da kasa sun sake yin roko da a wa Allah da Annabi a kara yawan taimakon kudi ga yankin da ke fama da masifar girgizar kasa a Pakistan. Wannan kiran ya zo ne gabanin wani babban taron kasashen duniya masu ba da agaji da zai gudana a birnin Geneva. Jami´an ba da agajin sun ce za´a shafe makonni kafin a kai taimako ga dubun dubatan mutane da suka makale a wasu kauyuka dake kan tsaunuka. Yanzu da ake fuskantar tsananin sanyin hunturu a yankin, har yanzu duniya ba ta da wani abin a zo a gani daga cikin taimakon da ake bukata ba. Daga cikin dala miliyan 312 da MDD ta nema da a taimakawa wadanda ke fama da bala´in girgizar kasar, miliyan 90 kadai aka bayar.