1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An saki dan Faransa da aka yi garkuwa da shi a Najeriya

November 17, 2013

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya tabbatar da sakin wani Inginiya dan kasar da ake garkuwa da shi tun cikin watan Disamba a Tarayyar Najeriya.

https://p.dw.com/p/1AJ4e
Hoto: Quentin Leboucher/AFP/Getty Images

A cikin wata sanarwar da shugaban ya fitar ya yi godiya wa mahukuntan Najeriya da suka taimaka aka sako Francis Collomp dan shekaru 63 da haihuwa, amma babu wani karin bayani kan yadda aka samu nasarar.

Sanarwar ta kara da cewa Shugaba Hollande ya umurci Ministan harkokin wajen kasar Laurent Fabius, ya kama hanyar tafiya Najeriya nan take, domin karbar Francis Collomp, wanda kimanin 'yan bindiga 30 suka yi garkuwa da shi a Jihar Katsina da ke yankin arewacin kasar. Ana daura alhakin garkuwa da mutane a arewacin kasar ta Najeriya kan kungiyar Boko Haram mai gwagwarmaya da makamai. Kuma kungiyar Ansaru da ta balle daga Boko Haram ta daukin alhakin wannan garkuwar.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito wata majiya tana cewa, Collomp ya samu kubuta sakamakon farmakin da dakarun Najeriya suka kaddamar kan Boko Haram.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Zainab Mohammed Abubakar