An salami Malala Yousufzai daga asibiti
January 4, 2013Talla
Matashiyar yar kimanin shekaru15 wacce ke goyon bayan tsarin illimintar da yan mata, an kwantar da ita ne a asbitin Queen-Elizabeth Hospita dake a Birmingham a tsakiyar kasar Ingila.
A cikin wata sanarwa da likitocinta suka baiyana sun ce ya zuwa yanzu jiginta yayi dama so sai; kafin a sake yi mata wani aikin tiyata a cikin sabon watan mai shirin kamawa.
A cikin watan Oktoban da ya gabata ne yan ƙungiyar Taliban suka harbi yariyar a wani harin da aka kai akan wata motar bus ta yan makaranta a garin Swat da ke a yankin arewa maso gabashin Pakistan ɗin.
Mawallafi : Abdourahamane
Edita : Umaru Aliyu