1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sanar da sabbin 'yan majalisar EU

Zulaiha Abubakar MNA
September 10, 2019

Sabuwar shugabar Hukumar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen, ta sanar da sunayen wasu jami'an da za ta yi aiki da su a majalisar gudanarwar hukumar.

https://p.dw.com/p/3PM8C
Belgien EU Kommission Ursula von der Leyen
Hoto: Reuters/Y. Herman

Ursula von der Leyen ta bayyana Phil Hogan a matsayin wanda zai jagoranci harkokin kasuwanci yayin da Paolo Gentiloni, tsohon Firai Ministan kasar Italiya zai jagoranci bangaren tattalin arziki.

Haka nan ta nada Margrethe Vestager a matsayin wacce za ta ci gaba da rikon mukamin kwamishinar gogayyar kasuwanci, ita kuwa Vera Jourova wacce ke rike da mukamin kula da daidaiton jinsi ta samu kari da mataimakiyar shugabar hukumar mai kula da bangaren dokoki.

A share guda kuwa, Ursula von der Leyen ta ce ficewar Birtaniya daga EU ba za ta raba alakar kasar da kungiyar ba. 

Shalkwatar hukumar mai ma'aikatan da yawansu ya kai dubu 33 na birnin Brussels na kasar Beljiyam.