1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben Najeriya: An soma bayyana sakamon zabe a wasu Jihohin

Abdourahamane Hassane
February 23, 2019

Rahotanni daga Najeriyar na cewar an rufe ciboyin zabe da dama a wasu sasan kasar inda tuni aka soma kidayar kuri'u, yayin da wasu kungiyoyin suka ce an kashe mutane 16 a tashin hankalin da ya barke lokacin zaben.

https://p.dw.com/p/3DwvI
Nigeria Präsidentschaftswahlen Schlange vor Wahllokal
Hoto: Getty Images/AFP/L. Tato

Rahotanni sun tabbatar da cewar a wasu jihohin Najeriyar an soma kidayar kur'i'u. Tun farko dai wata kungiyar masu saka ido  a shafinta na Twitter, ta ce an samu tsaiko bisa rashin isowar jami'an hukumar zaben da kuma matsaloli na ko rashin aikin na'aurar tantance bayanai ta card reader da tambari da dai sauransu. Jihohin da aka samu wadannan matsalolin sun hada da Akwa Ibom da ke kudancin kasar da kuma Legas, birni mafi girma a Najeriyan har ma da Jihar Kano.