1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar Hong Kong na kara zafi

Zulaiha Abubakar
September 7, 2019

Mahukuntan yankin Hong Kong sun umarci takaita jigilar fasinja tare da sanya tsattsauran tsaro a harabobin  filayen jiragen saman yankin, yayin da masu zanga-zanga suka fara lalata kayan gwamnati.

https://p.dw.com/p/3PChp
Hongkong Proteste gegen China PK Carrie Lam
Hoto: Reuters/Kim Kyung-Hoon

Jami'an 'yan sanda sun sanya shinge a tashoshin jiragen kasa da motocin haya don samun gudanar da binciken kwakwaf a fadin yankin. A ranar  Larabar da ta gabata ne jagorar yankin Carrie Lam ta sanar da shirin janye dokar da ta haifar da sabani tsakanin gwamnati da mazauna yankin, yunkurin da masu zanga- zangar suka yi watsi dashi.

Daga cikin shugabannin da suka sanya baki domin kawo karshen wannan danbarwa dai har da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel  wacce ta jaddada bukatar martaba 'yancin al'ummar yankin na Hong Kong yayin ziyarar da take a yanzu haka a China.