1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An umarci masu zanga-zanga da su bar fadar shugaban Masar

December 6, 2012

Rundunar sojin Masar ta ba 'yan adawa da kuma masu goya bayan shugaba Muhammad Mursi umarni da lallai su fice daga wajen da fadar shugaban kasar inda su ke zanga-zanga.

https://p.dw.com/p/16wmG
Supporters of Egyptian President Mohammed Morsi clash with anti-Morsi protesters outside the Egyptian presidential palace on December 5, 2012 in Cairo, Egypt. Islamist supporters of Egypt's President Mohamed Morsi chased opposition protesters away from the presidential palace, as the vice president said a vote on a controversial charter would go ahead as planned. AFP PHOTO/GIANLUIGI GUERCIA (Photo credit should read GIANLUIGI GUERCIA/AFP/Getty Images)
Proteste in Ägypten gegen Präsident MursiHoto: GIANLUIGI GUERCIA/AFP/Getty Images

Gabannin wannan sanawar dai jagoran jami'iyyar 'yan uwa Musulmi ta shugaba Mursi ya yi kira ga bangarorin biyu da su kai zuciya nesa domin tashin hankali ba zai haifawa kasar da mai idanu ba yayin da kasahsen Burtaniya da Amurka su ka nuna damuwarsu dangane da tada kayar bayan inda su ka shawarce su da sasanta.

Nan gaba ne dai a yau ake sa ran Shugaba Mursi zai yi jawabi ga al'ummar kasar sai dai fadar shugaban kasar ba ta tantance kan abubuwan da jawabin na shugaban zai maida hankali a kai ba.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Muhammad Nasir Awal