1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yanke hukuncin kaso ga shugabannin FDLR

Umaru Aliyu/GATSeptember 28, 2015

Kotun birnin Stuttgart na kasar Jamus ta yanke hukuncin zaman kaso na shekaru ga tsaffin shugabannin Kungiyar 'yan tawayen Ruwanda ta FDLR su biyu

https://p.dw.com/p/1GenJ
Deutschland Prozess gegen mutmaßliche Kriegsverbrecher der ruandischen Rebellenorganisation FDLR
Hoto: picture-alliance/dpa/D. Calagan

Bayan shari'a ta lokaci mai tsawo, a wannan Litanin wata kotu a birnin Stuttgart dake nan Jamus, ta zartas da hukunci kan wasu 'yan kasar Ruwanda biyu, saboda laifukan da suka hada har da goyon baya da taimakon aiyukan tarzoma da kuma kokarin da suka yi na kai hare-haren ta'addanci a wata kasar daban. Duka mutanen biyu dai manyan shugabanni ne na kungiyar yan tawaye ta FDLR da ta yi gwagwarmayar neman 'yanto kasar Ruwanda, wato Ignace Murwanashyaka da kuma Straton Musoni, sun dade suna zaune a Stuttgart, inda aka yi zargin cewar daga can ne suka rika tafiyar da aiyukan kungiyoyin da suke taimakawa domin aiyukan tarzoma.

Ruanda Deutschland Ignace Murwanashyaka im Gerichtssaal in Stuttgart
Hoto: picture-alliance/dpa/MDR/Fakt

Sakamakon hukuncin kotun Stuttgart

Alkali Juergen Hettich dake zartas da hukuncinsa, ya ce Straton Musoni, wanda ya shugabanci kungiyar ta FDLR, zai je gidan kaso har tsawon shekaru takwas, yayin da Ignace Murwanashyaka, aka zartas da hukuncin daurin shekaru 13 a kansa. Duk da haka, alkali Hettich ya ce Musoni ba zai ci gaba da zama a kurkuku ba, saboda tsawon lokacin da ya dauka a gidan kaso din kafin a yi shari'a da zartas da hukunci a kansa. Gaba daya mutanen biyu an zargesu da laifin hada baki da kuma hannu a yakin basasa a yankin gabashin Kwango tsakanin shekara ta 2008 zuwa 2009, inda mutane masu yawa suka rasa rayukansu, mafi yawansu farar hula. A lokacin da yake maida martani a game da wannan hukunci kan 'yan kasar ta Rwanada biyu a Stuttgart, ministan shari'a kuma antone-janar na Ruwanda, Johnson Busingye, ya ce wannan hukunci matakin farko ne kawai na tabbatar da hakkin wadanda suka mutu ko suka tagaiyara sakamakon aiyukan rashin imani na 'yan Kungiyar FDLR.

Martanin gwamnatin Ruwanda kan hukuncin kotun

"Ya ce tun bayan kisan kare dangi da aka yi a Ruwanda a shekara ta 1994, an gudanar da shari'o'i da taruka na neman sulhu masu yawa a kusan ko ina cikin duniya, an yi a Holland, an yi a Amirka, an yi a Afirka, ga kuma shari'a dake gudana a Stuttgart yanzu. To sai dai wannan shari'a a yanzu ta dauki hankalin duniya ne musamman saboda shugabannin Kungiyar FDLR ne suka gurfana gaban kotu. Hakan ya nuna wa duniya cewar masu aikata irin wannan laifi na kisan kare dangi ko laifukan yaki, cewar shari'a tana iya cimmasu a duk inda suke".

Straton Musoni, mutmaßlicher Mitverantwortlicher für den Völkermord in Ruanda
Hoto: picture-alliance/dpa/B. Weissbrod

Minista Busingye ya ce duk da haka, babban aikin dake gaban masu shari'a da wadanda rikicin ya shafa, shi ne na kawo karshen aiyukan Kungiyar FDLR a yankin gabashin Kwango. Kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ta yi marhabin da wannan hukunci, inda ta ce duniya yanzu dai ta zama yar karama, wadda babu sauran inda duk wadanda ake zarginsu da aikata manyan laifukan yaki ko kisan kare dangi ba su da wurin buya. Ko da shike kotun da ta zartas da hukuncin a Stuttgart nesa take da gabashin Kwango, amma ta sami nasarar zartas da hukuncin da ya dace da hakkin dubban 'yan Kwango da suka sha wahala daga aiyukan kungiyar ta FDLR. Ita ma Cibiyar kare hakkin democradiya da 'yancin dan Adam ta kasashen Turai dake Berlin ta ce ta gamsu da wannan hukunci na Stuttgart. Janar sakatarenta, Wolfgang Kaleck ya ce sakamakon shari'a da hukuncin da aka zartas a Stuttgart kan 'yan Ruwandan biyu, Jamus ta bada gudummawarta ga farauta da hukunta masu sana'ar keta hakkin 'yan Adam da laifukan yaki da kisan kare dangi a duniya baki daya.