An yanke wa Oscar shekaru biyar
October 21, 2014A yau Talata ce dan wasan nakasassunnan dan kasar Afirka Ta Kudu Oscar Pistorius ya san hukuncinsa na zaman shekaru biyar a gidan kaso bayan kisan masoyiyarsa a ranar masoya ta shekarar bara.
A cewar me shari'a masifa zai kwashe wadannan shekaru ne saboda kisa ba da ganganba, hukuncin da ya kawo karshen watanni bakwai na bibiyar wannan shari'a da ta dauki hankula na al'umma a kasashen duniya.
A yau dai mai shari'a Thokozile Masipa, ta yanke nata hukuncin, bayan da a baya mai gabatar da kara ya nemi a daure Oscar Pistorious tsawon shekaru goma a gidan kaso, inda a bangaren masu ba shi kariya ke neman a yi masa daurin talala a gida, sannan ya rika wasu ayyuka na taimakon al'umma.
A watan da ya wuce ne mai shari'a Masipa ta sami Oscar da laifin kisan budurwarsa Reeva Steenkamp, amma ba da ganganci ba, laifin da zai iya sawa a yi masa hukunci da ya kama daga tara zuwa dauri a gidan kaso.