1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yanke wa 'yan IS hukuncin kisa a Libya

May 29, 2023

Kotun daukaka kara a kasar Libiya ta yanke hukuncin kisa a kan wasu 'yan kungiyar IS mutum 23 bisa kamasu da laifi kaddamar da wasu munanan hare-hare a shekarun baya a kasar.

https://p.dw.com/p/4Rwfm
Syrien Irak Islamischer Staat (IS)
Hoto: Dabiq/Planet Pix via ZUMA Wire/ZUMAPRESS/picture alliance

Kotun wacce ta yi zamanta a birnin Misrata ta kuma yanke wa wasu mutum 14 hukuncin daurin rai da rai, yayin da wasu karin mutanen 9 suka sami hukuncin tsakanin shekaru 3 zuwa 12.

Tun bayan rikicin shekarar 2011 wanda ya yi sanadiyar kifar da gwammantin Muammar Gaddafi kungiyoyin IS da wasu masu tsatsauran ra'ayin addini suka karbe iko da birnin Sirte, wanda ke zama mahaifa ga tsohon shugaban.

Daruruwan 'yan kungiyar ta IS na kulle a kurkuku tun bayan da asojojin gwamnati suka ci karfinsu, inda da damansu ke jiran shari'a.