1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bankwana da Kofi Annan a Ghana

September 13, 2018

A wannan Alhamis ce aka binne gawar Kofi Annan tsohon sakataren Majalisar Dinkin Duniya a kasarsa ta asali wato Ghana bayan bikin ban-kwana da shugabanni suka yi masa.

https://p.dw.com/p/34mve
Kofi Annan ist verstorben
Hoto: Getty Images/AFP/S. Bozon

Al'ummar kasar Ghana da sauran na sassan duniya sun yi jimami a wannan Alhamis da aka binne gawar tsohon sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan a kasarsa ta haihuwa wato Ghana, bayan bikin ban-kwana da shugabanni dabam-dabam suka yi masa. Bikin binne Mr. Annan wanda aka yi da misalin karfe 8.30 na safiyar Alhamis  agogon Ghana, shi ne zai kawo karshen girmamawar da kasar ta shirya masa.

Ghana Beisetzung Kofi Annan
Taron addu'ar ban kwana da Kofi Annan a GhanaHoto: Getty Images/AFP/C. Aldehuela

Marigayin ya jagoranci Majalisar Dinkin Duniyar ce tsakanin shekarar 1997 zuwa 2006, mukamin da ya kasance bakar fata na farko da ya rike shi. Kofi Annan ya bar duniya ne a ranar 18 ga watan jiya na Agusta yana da shekaru 80, bayan gajeriyar jinya da ya yi a kasar Switzerland.

Ghana Beisetzung Kofi Annan, Antonio Guterres
Antonio Guterres na MDD na cikin manyan baki a bikin binne AnnanHoto: picture alliance/AP Photo

Da take jawabi a wajen bikin binne mamacin 'ya ga Annan ta bayyana mahaifinta a matsayin mutum mai saukin kai da ke jan hankali ga iyalansa su zama masu takawa da yawan godiya ga mahalicci.

Bikin binne Annan ya samu halartar manyan baki a ciki da wajen kasar ta Ghana, musamman jami'ai da ke zama na diflomasiya a wannan lokaci da lokutan baya wadanda suka rika bayyana kyawawan halaye na mamacin da ke zama gwarzo a Afirka.