1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi ganawa ta farko a Geneva

Abdourahamane HassaneFebruary 1, 2016

Wakilan 'yan adawa na Siriya sun gana da manzon musammun na MDD Staffan de Mistura a ci gaban tattaunawar da ake yi a domin samar da hanyoyin kawo ƙarshen yaƙin Siriya.

https://p.dw.com/p/1HnI8
Genf Syrien Konferenz Staffan de Mistura
Hoto: picture alliance/dpa/M. Trezzini

Majiyoyin diplomasiya sun ce buƙata ɗaya daga cikin buƙatun da 'yan adawar suka gabatar ita ce ta ganin gwamntin Bashar al Assad ta sako dubban fararan hula da take tsare da su a gidajan kurku:

Bayan wannan ganawa an shirya mista de Misura zai gana da tawagar jami'an gwamnatin Siriya;Kuma yanzu haka jama'a ƙasar ta Siriya da dama na jiran ganin irin sakamakon da za a cimma a wannan taro.