1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi garkuwa da mutane a birnin Sydney

Ahmed SalisuDecember 15, 2014

Rahotanni na cewar wani dan bingida ko 'yan bindiga sun yi garkuwa da mutanen da ba a tantance adadinsu ba wajen wani shan shayi da ke birnin Sydney na kasar Austreliya.

https://p.dw.com/p/1E47m
Australien Geiselnahme in Sydney 15.12.2014
Hoto: Reuters/J. Reed

Wani dan bindiga a birnin Sydney na kasar Austreliya ya yi garkuwa da mutane da dama a wajen wani shan shayi, batun da ya sanya jami'an tsaro da dama yin damarar yaki inda suka yi wa wajen kawanya da ma dakartar da zirga-zirgar jama'a a akasarin yankunan birnin.

Guda daga cikin manyan jami'an 'yan sandan Austreliya ya ce jami'an tsaron da ke wajen kwararru ne da suka samu horo kan irin wannan yanayi kuma ya na fatan aikin da suke zai haifar da sakamako mai kyau.

Masu aiko da rahotanni dai na cewar mutanen da ake rike da su din sun dafa hannayensu a jikin wata taga da ke dauke da wata bakar tuta mai rubutun larabci, yayin da wasu biyar daga cikinsu ciki kuwa har da ma'aikatan wajen suka samu kubuta.

Firaministan Austreliya Tony Abbot ya ce suna hasashen cewar garkuwa da mutanen da aka yin yana da nasaba da siyasa, inda a hannu guda ya jajanta wa iyalan wanda abin ya ritsa da su.