1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi jana'izar 'yan ciranin Najeriya

Ramatu Garba Baba
November 18, 2017

Mahukuntan kasar Italiya sun sanar da gudanar da jana'izar wasu 'yan ciranin Najeriya guda ashirin da shida da suka rasa rayukansu a sanadiyar hadarin jirgin ruwa a tekun Mediterranean.

https://p.dw.com/p/2nsMC
Libyen Tripoli Küstenwache gerette Migranten
Hoto: Reuters/H. Amara

An binne gawarwakin a wata makabarta da ke a kudancin kasar ta Italiya, mutane akalla sittin ne aka rawaito cewa jirgin ruwan da suke tafe a ciki ya nutse da su a tsakiyar tekun, sai dai wadanda suka mutun duk mata ne masu shekaru tsakanin goma sha uku da ashirin. An gudanar da jana'izar a jiya ne a gaban wasu daga cikin 'yan uwan mamatan da suka yi nasarar tsira daga hadarin jirgin ruwan bayan da suka baro kasar Libiya cike da burin tsallakawa Turai. 

A yayin da kasashen duniya ke cewa suna kokarin magance wannan matsala ta mutuwar 'yan cirani, alkaluma na cewa akalla mutane dubu uku ciki har da mata da kananan yara ne suka rasa rayukansu a bana kawai, a yayin da suke kokarin tsallakawa zuwaTurai.