1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bukaci 'yan asalin kasar Iraki su koma gida

Zulaiha Abubakar MNA
December 19, 2018

Ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas ya baiyana cewar 'yan gudun hijirar kasar Iraki za su iya komawa gida a halin yanzu biyo bayan nasarar kawo karshen kungiyar IS a kasar.

https://p.dw.com/p/3AMFj
Heiko Maas, Mohammed Ali al-Hakim
Hoto: picture-alliance/K. Kadim

Ministan harkokin wajen na Jamus Heiko Maas ya kuma kara da cewar duba da yadda harkokin tsaro suka inganta a Iraki, 'yan kasar masu zaman gudun hijira a Jamus za su iya komawa don ci gaba da rayuwa a kasarsu. Ministan ya baiyana hakan ne a ranar Talatar da ta gabata yayin da ya kai ziyara Iraki.

Da yake tofa albarkacin bakinsa kan wannan batu ministan harkokin wajen Iraki Mohammed Ali al-Hakim kira ya yi da 'yan asalin kasar da ke zaman gudun hijira a kasashe dabam-dabam na duniya da su dawo gida don ciyar da kasar gaba.